Kotun sojin Mali ta ce an kama sojojin ƙasar da dama kan zargin hannu a hare-haren ƴanbindiga masu alaƙa da al-Qaeda da ƴantawayne Tuareg a makon da ya gabata a faɗin ƙasar.
Masu shigar da ƙara sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma tuni binciken ya gano hannun wasu sojojin ƙasar da kuma waɗanda suka yi ritaya wajen kisat hare-haren.
Cikin wata sanarwa da sojojin mulkin ƙasar suka karanta a gidan talbijin na ƙasar, ba su bayayana adadin sojojin da ke da hannu a hare-haren ba, amma ta tabbatar da ƙarin kame cikin rundunar sojin ƙasar, yayin da ake ci gaba da bincike.
Haka ma ana zargin ‘yansiyasar ƙasar, ciki har da jagoran adawar ƙasar da ke zaman gudun hijira a wajen ƙasar, Oumar Mariko.
A lokacin hare-haren na makon da ya gabata an kashe ministan tsaron kasar.
Yanzu haka dai ‘yanbindigar sun ce suna shirin yi wa Bamako, babban birnin ƙasar ƙawanya, yayin da rahotonnni suka ce tuni mayaƙan sun fara kafa shingayen bincike a faɗin birnin.
