Wasu magoya bayan tsohuwar jam’iyyar NDC sun zargi shugabannin jam’iyyar da nuna rashin adalci, lamarin da suka ce ne ke haifar da yunƙurin da Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, ke yi na ficewa daga jam’iyyar.
Jagoran matasan jam’iyyar na ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, Ambasada Saminu Shehi Kura, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce akwai buƙatar shugabannin jam’iyyar su sake duba tsarin gudanarwarta tare da bai wa mambobin tsohuwar NDC cikakken adalci kafin su ɗauki matakin da zai iya shafar makomar jam’iyyar.
Ambasada Saminu Shehi Kura ya kuma yi barazanar cewa za su ƙaurace wa zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabi’u Musa Kwankwaso, idan har ba a bai wa mambobin tsohuwar NDC kaso 40 cikin 100 na kujerun takara ba.
Ya ƙara da cewa rashin adalci a cikin jam’iyyar na iya jawo mata matsala a zaɓe, yana mai kira ga shugabanni da su gaggauta warware rikicin cikin gida domin tabbatar da haɗin kai da samun nasara a zaɓuka masu zuwa.
