Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Whirl Stroke, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron al’umma na Jihar Benue, sun kashe wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar ranar 16 ga Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan maboyar waɗanda ake zargin.
Sanarwar ta ce dakarun sun bi ta Takum da ke Jihar Taraba zuwa ƙauyukan Tse Togo da Utenge, kusa da sansanin Orter, inda aka yi zargin masu garkuwa da mutane ke amfani da wurin a matsayin mafakarsu.
Rundunar ta bayyana cewa mutanen uku da aka ceto duk mazauna Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ne, yayin da wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su suka samu damar tserewa daga sansanin a lokacin musayar wuta tsakanin sojoji da waɗanda ake zargin.
Haka kuma, sojojin sun ƙwato makamai, harsasai da sauran kayayyakin aikin soja da ake zargin ‘yan ta’addan ke amfani da su.
Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da hare-haren da suka dace domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
