Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Kano Ta Tabbatar da Gano Illar Bata Tarbiyya Yara Mata a...

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Gano Illar Bata Tarbiyya Yara Mata a Shirin Tallafawa Ilimi Na AGILE

Date:

Biyo bayan zarge-zargen bata tarbiyya da ake yiwa shirin tallafawa ilimin yaya mata na AGILE, ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta gudanar da taron karawa juna sani na yini biyu kan shirin.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda ya yi magana a yayin taron na masu ruwa da tsakin da ke nazarin horar da dabarun rayuwa a karkashin shirin, ya ce ma’aikatar ta fitar da wani sabon salo na abubuwan da shirin ya kunsa.

Ya ce malamai sun yi korafin cewa a cikin shirin akwai wasu abubuwa da basu amince da su ba inda suka duba korafin nasu kuma suka gano matsalar dake cikin sa yayin da aka cire duk wani da ya saba da al’ada da koyarwar addnini muslunci.

A nashi bangaren, co’odinetan shirin na AGILE a nan Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi-Kwalli, ya ce makasudin bitar shirin shi ne duba shi da yin nazari da gyara domin samar da ingantaccen tsarin koyarwa na addinin Musulunci da zamantakewa a jihar Kano.

Ya ce za a fassara abubuwan da shirin ya kunsa da aka gudanar a yayin taron zuwa harshen Hausa da Larabci domin kowane mai ruwa da tsaki ya ga irin abin da ake koyawa yara matan.

AGILE wani shiri ne da ke samun tallafin bankin duniya domin inganta ilimin yan mata masu tasowa a makaratun sakandare, sai dai an yi ta zargin akwai manufa ta bata tarbiyya a cikinsa har ta kai sarkin Katsina, ya bayar umarnin dakatar da shirin a jihar a makon da ya gabata.

Latest stories

Related stories