Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMun samar da babura dari bakwai da talatin, domin rabawa jami'ansa kai...

Mun samar da babura dari bakwai da talatin, domin rabawa jami’ansa kai na banga – Gwamnatin Jihar Kebbi

Date:

Gwamnatin jihar Kebbi ta samar da babura dari bakwai da talatin, domin rabawa jami’ansa kai na banga, domin su rika taimakawa jami’an tsaro wajen sintiri don yaki da matsalar rashin tsaro.

Gwamnan jihar Kebbi, Dokta Nasir Idris, ya bayyana cewa an samar da baburan ne domin ‘yan banga su rika taimakawa jami’an tsaro na hukuma wajen samar da tsaron jihar ta Kebbi.

Shugban kungiyar ta banga a jihar Sanusi Ibrahim Geza ya ce samar da babran faduwa ce ta zo daidai da zama, domin da ma baburan ne su ke bukata kuma sun samu wadanda ma suka fi wadanda barayin daji ke amfani da su.

Ibrahim Geza, ya tabbatar da cewa, jami’ansu sun hallaka masu satar mutane a karamar hukumar Ngaski da Danko Wasagu, da kuma wani jagoran masu garkuwa da mutane a yankin Bunza da Kalgo mai suna Dogo Oro.

Tun bayan da gwamnonin jihohin arewa maso yamma suka hadu, tare da daukar kudurin yin aiki tare don shawo kan matsalar rashin tsaro, har yanzu ana samun rahotannin kai hare-hare a wasu jihohi, abin da ke nuna tsugunne bata kare.

Latest stories

Related stories