Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaKungiyoyin dake makarantun gaba da sakandire sun yi amanna da yadda gwamnatin...

Kungiyoyin dake makarantun gaba da sakandire sun yi amanna da yadda gwamnatin tarayya ta cire jamioi, kwalejojin fasaha da na ilimi daga tsarin IPPIS

Date:

Kungiyoyin dake makarantun gaba da sakandire sun yi amanna da yadda gwamnatin tarayya ta cire jamioi, kwalejojin fasaha da na ilimi daga tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS wajen biyan maaikatansu albashi da alawus-alawus.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, a zantawarsa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja ne ya bayyana cire manyan makarantun daga wancan tsari da ya haifar da rashin jituwa tsakanin kungiyoyin maaikatan manyan makarantun da gwamnatin tarayya, inda suka rika shiga yajin aiki domin ganin a dakatar dashi.

A tattaunawar sa da premier radio, shugaban kungiyar malaman jamioin shiyyar Arewa, Dr Abdulkadir Muhammad Dambazau ya ce sun yabawa gwamnatin tarayya kan daukar wannan mataki tare da kira da ta gaggauta magance sauran korafe korafen da suka gabatar mata.

Suma kungiyar kwalejojin ilimi ta tarayya ta bakin shugaban kungiyar kwalejen ilimi ta Bichi Dr hussaini Yahaya Tani yabawa gwmantin su ka yi inda suka ce da wannan tsarin ya kawo matsaloli da dama a tafiyar da harkokin manyan makarantu.

A jiya ne dai Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja,ya bayyanawa manema labarai cewa gwamnatin tarayyar ta cire manyan makarantun daga tsarin na IPPIS.

Latest stories

Related stories