Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAASG: Kwanaki 100 sunyi wuri a kalubanci mulkin  shugaba Bola Tinubu a...

AASG: Kwanaki 100 sunyi wuri a kalubanci mulkin  shugaba Bola Tinubu a kasar nan

Date:

Gamayyar kungiyoyin sakai na APC sunce yayi wuri ace tun yanzu al’umma sun fara yankewa shugaba Bola Ahmad Tinubu hukunci kan yadda yake mulkin kasar nan.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnonin kasar nan da ministoci

Shugaban gamayyar kungiyoyin na(Amalgamated APC Support Group AASG) Injiniya Salisu Magaji, ne ya bayyana haka yayin ganawar sa da manema labarai.

Injiniya Salisu ya ce kamata yayi al’umma su baiwa gwamnatin Tinubu a kalla watanni shida kafin yi mata alkalanci.

Ya ce irin aikace aikacen da Tinubu yayi lokacin da yake gwamna a jihar Lagos ya tabbatar da cewa zai kai kasar nan ga ci.

Ya ce daga hawan sa kan mulki ya fara inganta harkar tsaro wanda ada mutum ba zai iya zuwa Abuja a mota ba sabanin yanzu.

Jami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu

“kuma ko yanzu kaga yadda masu zuba jari ke tururuwar dawowa kasar nan domin zuba jari

Matsalar tsaro matsala ce ta duniya baki daya kuma lokaci ne yanzu da kowa zai bada gudunmawar sa wajen magance matsalar,” a cewar sa.

Injiniya Salisu Magaji ya kuma ce ba gaskiya bane batun da ake cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bata bar komai a asusun kasar nan dake waje ba.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...