Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeAl'aduDaliban da gwamnatin Kano zata dauki nauyi zasu fara karatu a watan...

Daliban da gwamnatin Kano zata dauki nauyi zasu fara karatu a watan Satumba

Date:

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace ɗaliban da gwamnatinsa zata ɗauki nauyin karatun digirinsu na biyu zasu fara harkokin karatunsa a watan Satumba na wannan Shekarar.

Gwaman ya bayyana hakan ne lokacin da karɓi bakuncin Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya kai masa ziyarar barka da Sallah a gidan gwamnatin kano.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na baiwa Ilimi fifiko, Inda yace daga hawansa kan mulki ya sake buɗe makarantu 20 da gwamnatin data gabata ta rufe , hadi da bude makarantun koyar da harkokin addinin musulunci na kananan hukumomin 44 dake jihar kano domin samar da ingantaccen ilimi ga al’umma.

Gwamna Abba Kabir ya kuma yaba da irin rawar da sarakunan gargajiya suka tawa wajen Adana tarihi da al’ada da bunkasa zaman lafiya da cigaba a jihar kano.n

A nasa jawabin Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce ya kai ziyarar ne domin yiwa gwamnan Barka da Sallah, sannan ya bukaci gwamnatin jihar ta samar da taki ga manoma don inganta harkokin noma a kano.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...