Saurari premier Radio
27.6 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNottingham Forest ta nuna sha'awar daukar Kelechi Iheanacho daga Leicester City. 

Nottingham Forest ta nuna sha’awar daukar Kelechi Iheanacho daga Leicester City. 

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest ta nuna sha’awar daukar dan wasan Super Eagles Kelechi Iheanacho daga Leicester City.

Forest na fatan kara karfafa ‘yan wasan Nottingham bayan samun nasarar ci gaba da buga gasar Firimiya.

Idan kuma Iheanacho ya koma Nottingham Forest zai hadu da sauran takwarorinsa ‘yan Najeriya da ke wasa a can kamar su Ceyril Dennis, da Taiwo Awoniyi da ya jefa kwallo tara a gasar Firimiya ta bana.

Bayan komawar Leicester City gasar ‘yan dagaji ta Championship, Iheanacho zai yanke shawarar barin kungiyar.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories