Saurari premier Radio
27.6 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoYunusa Yellow ya shaki iskar yanci daga gidan gyaran hali

Yunusa Yellow ya shaki iskar yanci daga gidan gyaran hali

Date:

Matashin nan Yunusa Yellow ya shaki iskar yanci daga gidan gyaran hali a jihar Kano.

Matashin da kotu tayiwa hukunci sakamakon auren wata matashiya ba bisa ka’ida ba ya kammala zaman gidan kaso a wannan rana.

Abaya dai Yunusa Yellow ya fara zaman gidan kaso a Jihar Bayelsa Kafin Daga Bisani a maido Dashi Jihar Kano bisa yadda wasu rukunin masu fada aji da lauyoyi suka shige gaba kan batun shari’ar tasa.

Yayin tattaunawa da manema labarai mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali na Jihar Kano Musbahu Kofar Nasarawa ya tabbatar da sakin matashin.

Kakakin hukumar gyaran halin na Kano ya ce bayan dawowar Yunusa Yellow Kano ya samu kyakyawar shaida wurin gudanar da rayuwarsa a gidan.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories