Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane 10 Tare Da Ta Talata Gidaje Sama...

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane 10 Tare Da Ta Talata Gidaje Sama Da 200 a Jihar Katsina.

Date:

Rahotanni daga jihar Katsina sun ce mutane 10 sun mutu yayin da gidaje sama da 200 da tituna suka lalace a unguwannin dake babban birnin jihar da kuma karamar hukumar Bindawa sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka.

Mazauna yankunan dai sun yi ta kokarin kwashe kayansu daga gine-ginen da ambaliyar ruwan ta shafa, bayan saukar ruwan samar kamar da bakin kwarya da yammacin ranar Talata har zuwa daren ranar.

Mai unguwar yankin, Alhaji Yunusa Suleman Rico, ya shaidawa manema labarai cewa mutane 10 ne suka mutu a iftila’in, ciki har da wani jariri da ba a gano gawarsa ba.

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon toshewar magudanar ruwa a unguwannin da lamarin ya shafa, wanda hakan ya hana ruwan tafiya daga Kofar Kaura.

To sai dai wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ta ce mutane biyu ne suka mutu sakamakon iftila’in.

Ya kuma jajantawa wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya ce tuni aka fara kokarin shawo kan lamarin tare da hana afkuwar haka a nan gaba.

Latest stories

Related stories