Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje yace ya gina shaguna a filayen Gwamnati domin ya bunkasa tattalin...

Ganduje yace ya gina shaguna a filayen Gwamnati domin ya bunkasa tattalin arzikin Kano

Date:

Tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayi karin bayan akan muhimmancin gine ginen shagunan da yayi a lokacin mulkinsa.

Yace an samar da tsarin gina shagunan ne, domin baiwa yan kasuwa damar baiwa tattalin arzikin Kano gudunmawa, ta hanyar samar da wuraren da kudin su.

Yace bisa tsarin yarjejeniyar ce, jihar ta sami karin kudin shiga na miliyoyin naira, wanda ya taimakawa wajen samar da ayyukan more rayuwa ga jama’a.

Ganduje ya bayyana takaicin yadda gwamnati mai ci ke rushe shagunan, musamman ma ganin yadda al’umma ke tafka asara, baya ga barnatar da dukiya ba gaira ba dalili da yace ana yi.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...