Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoShagunan da Ganduje yayi a filin idi suna kawo barazana ga tsaron...

Shagunan da Ganduje yayi a filin idi suna kawo barazana ga tsaron masallata -Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya alakanta matakin rushe shagunan filin idi a Kano da sha’anin tsaron masallata.

A zantawarsa da yan jarida bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu, Kwankwaso ya ce a lokacin gwamnatinsa, sai da aka yiwa filin Idin shinge da gilashi mai silke, domin kyautata tsaron wurin.

To sai dai yace gine ginen shagunan da gwamnatin magajinsa Abdullahi Umar Ganduje ta yi, na barazana ga tsaron hakan yasa Gwamna Abba Kabir Yusuf yaga dacewar rushe gine-ginen.

Gwamna Abba Kabir ya fara rushe dukkan gine-ginen da akayi ba bisa ka’ida ba a filayen Gwamnati Jim kadan bayan rantsar dashi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories