Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Monday, April 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDSS ta kama tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele

DSS ta kama tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele

Date:

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi ram da tsohon shugaban babban bankin kasa CBN, Godswin Emefiele.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan sanar da dakatar dashi daga mukaminsa.

Idan za a iya tunawa, tun a ranar 7 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, hukumar ta DSS ta nemi izinin kama Emefiele, bisa zargin daukar nauyin yan ta’adda, ha’inci da kuma laifukan da suka shafi cin dunduniyar tattalin arzikin kasa.

To sai dai, a wancan lokacin, alkalin babbar kotun tarayya, Justice John Terhemba Tsoho, ya nemi a sake gabatar da bukatar bisa sahalewar shugaban kasa, domin kaucewa jefa tattalin arzikin kasar nan a wani hali.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories