Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje bai Isa yayi mun wani abu ba- Kwankwaso

Ganduje bai Isa yayi mun wani abu ba- Kwankwaso

Date:

Tsohon dan takarar shugaban kasa Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kalaman tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje barazana ce kawai amma babu wanda ya isa yayi masa wani abu.

Kwankwaso ya ce bacin rai ne yasa Ganduje ya ce zai iya marin sa da ace sun hadu a fadar shugaban kasa.

A ranar Juma’a ne dai tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayi barazanar marin Kwankwaso da sun hadu a fadar shugaban kasa a cewar sa.

Sai dai Rabi’ u Musa kwankwaso ya ce duk mutum mai hankali zai yaba da matakin da gwamnatin Kano ta dauka na rushe gine-ginen da akayi ba bisa ka’ida ba.

Rabiu Musa Kwankwaso, ya kara da cewa sun tattauna da shugaban kasa Tinubu kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati domin samun nasarar.

Ya kuma tabbatar da cewa sun sake tattauna batun bashi mukami a sabuwar gwamnatin idan an samu yarjejeniya.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...