Saurari premier Radio
27.6 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDSS kawo yanzu ba ta tsare da tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele

DSS kawo yanzu ba ta tsare da tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele

Date:

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce yanzu haka ba ta tsare da tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar nan Godwin Emefiele.

A wani sako da hukumar DSS ta fitar a shafin ta na twitter tace yanzu haka Emefiele ba ya tare da su.

Tun a daren Juma’a wasu rahotanni sun ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

Ba wannan ne karon farko da rahotanni ke alaƙanta tsohon gwamnan da DSS ba, musamman tun bayan da ya ƙaddamar da shirin sauya takardun naira da kuma rage yawan garin kuɗin a hannun mutane bisa amincewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan bankin ne nan take cikin wata sanarwa, inda aka umarce shi da ya miƙa ragamar CBN ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi.

Mista Adebisi zai kasance muƙaddashin gwamna har sai an kammala binciken zarge-zarge a kan Emefiele da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...