Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Katsina ya goyi bayan takarar Akpabio da Barau a shugabancin majalisar...

Gwamnan Katsina ya goyi bayan takarar Akpabio da Barau a shugabancin majalisar dattawa.

Date:

 

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya goyi bayan da tsayar da Sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin wadanda za su shugabantci majalisar dattawa ta 10 ta kasa.

Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Malam Ibrahim Kaula, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Katsina.

A cewarsa, Radda ya bayyana goyon bayan sa ne a lokacin da Akpabio da Barau suka jagoranci tawagar yan majalisar dattawan kasar suka kai masa ziyarar ban girma a dakin taro na jihar Katsina, a Abuja.

Sanata Akpabio wanda tsohon gwamnan Akwa Ibom ne kuma tsohon ministan harkokin Neja Delta da kuma Sanata Jibrin mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, su ne jamiyyar APC ta zaba a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa.

Latest stories

Related stories