Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaLikitoci na gargadi kan shan ruwan gishiri da siga barkatai a watan...

Likitoci na gargadi kan shan ruwan gishiri da siga barkatai a watan Azumi

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Masana kiwon lafiya na gargadi ga al’umma game da amfani da sinadarin ruwan gishiri da suga a wannan lokaci na azumin watan Ramadan ba tare da amincewar likita ba.

Hakan ya biyo bayan wasu al’umma ke amfani da sinadarin a Lokutan buda baki da sahur barkatai ba tare da shawrar likita ba.

A zantawar wakilinmu Ahmad Adamu Yau da wani likita da ke jihar Yobe, Dakta Isma’il Hashim, ya ce wannan shan ruwan gishi da suga ba tare da umarnin likita ba, ya kan haifar da matsala.

Dakta Isma’il Hashim ya ce mutukar mutum ya na shan ruwan gishi da suga ba tare da shawarar likita ba, hakan ka iya haifar da cutar hawan jini da sauran cutuka.

Dakta Isma’il Shanono ya bukaci al’umma dasu kasance suna tu’ammali da abubuwa bisa shawarwarin masana domin gujewa kamuwa da cuta.

Wasu mazauna Kano sun bayyana cewa, suna amfani da sinadarin a matsayin wani abu da zai kara kuzari bayan kwashe tsawon lokaci ana ibadar azumi.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...