Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu Ta Sake Aikewa Dauda Rarara Sammacin Ya Gurfana A Gabanta.

Kotu Ta Sake Aikewa Dauda Rarara Sammacin Ya Gurfana A Gabanta.

Date:

Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake Rijiyar Zaki a jihar Kano, ta yi umarnin a sake rubutawa mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, sabon sammaci sakamakon rashin halattar zaman kotun.

Ana karar Rarara ne kan kin biyan wasu kudi kimanin Naira miliyan goma da dubu dari uku na cinikayyar wayoyin salula da yake karba a wajen wani dan kasuwa, Muhammad Ma’aji, ya na rabawa mutane.

Lauyan mai kara Barista I. Imam ya shaidawa kotun cewa, wanda ake karar bai mutunta sammacin da aka kai masa ba, dan kuwa bai halacci zaman kotun ba, don haka ya roki kotun da ta yi umarnin a kamo Rarara kasancewar ya raina kotu.

Barista I. Imam yace bai san ko sammacin da aka baiwa wanda ake karar ko ya isa gareshi ba.

Sai dai alkalin kotun mai shari’a, Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ya tambayi jami’in kotun da ya kai sammacin, Isma’il Zuhudu, ko ya ba Rarara hannu da hannu, inda ya ce ya like masa takardar ne a kofar gidanshi kamar yadda kotun ta yi umarni, sakamakon sun neme shi don ya ba shi hannu da hannu amma bai same shi ba.

Aljalin ya ce kasancewar wanda ake tuhuma bai zo ba kuma bai aiko ba, kotun ta yi masa uzuri saboda wannan ne karo na farko da ya yi haka, in da ya yi umarnin a sake rubuta sabon sammaci ga Rarara a sake kai masa ko kuma like a kofar gidanshi da ke kan titin Gidan Zoo a jihar Kano tare da wallafa sammacin a shafukan sada zumunta da kafafan yada labarai.

Kotun ta kuma sanya ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023 domin ci gaba da shari’ar.

Latest stories

Related stories