Saurari premier Radio
26.3 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta kama mutum 37 da laifin fataucin miyagun kwayoyi a Kano...

Kotu ta kama mutum 37 da laifin fataucin miyagun kwayoyi a Kano -NDLEA

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA, ta ce ta samu nasarar kama wasu masu fataucin miyagun kwayoyi 37 da masu da masu ta’ammali da su tsakanin watan Janairu zuwa Maris din wannan shekara.

Kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris Ahmad ne ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau litinin.

Ya ce baya ga mutane 37 da babbar kotun tarayya ta yanke wa hukunci, rundunar ta shigar da sabbin kararraki 39, yayin da sauran kararraki 127 ke gaban kotu.

Ya ce a tsakanin watan Janairu zuwa Maris, an kwace tabar wiwi da nauuinta ya kai 955.304kg, sai kuma hodar lblis mai nauyin 25kg da sauran miyagun kwayoyi da suka kama.

Ya kuma bukaci mazauna Kano da su baiwa hukumar bayanan ayyukan dillalan miyagun kwayoyi dake yawo a cikin al’umma.

Babban kwamandan na NDLEA a Kano yi kira ga sauran jama’a da iyaye da kuma shugabannin al’umma da su kasance masu lura da unguwanninsu domin magance matsalar fataucin miyagun kwayoyi da ta’ammali da su.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...