Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniDalilan da ya sa aikin hajjin bana ya yi tsada-Danbatta

Dalilan da ya sa aikin hajjin bana ya yi tsada-Danbatta

Date:

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce tsadar farashin Dala, a kasuwar duniya da masaukin alhazai a kasa mai tsarki ne ya sabba tsadar aikin Hajjin bana.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan ya yin da yake zantawa da manema labarai ranar juma’a.

Hukumar dai ta ayyana N2, 900,019 a matsayin kudin aikin Hajjin bana mai makon N2, 500,000 da aka biya a bara.

Muhammad Abba Danbatta ya ce a bana gwamnatin tarayya ta baiwa hukumar NAHCON canjin Dala akan N456 maimakon 410 da aka bayar a bara.

“Idan aka yi la’akari da abinda ya faru 2018 da 2019 gwamnati ta baiwa hukumar kula da aikin Hajji da Umar ta tarayyar Najeriya farashin Dala akan N305, a dubu 2018 kuma ta bayar akan N306.

“A 2022 da ta gabata an bayar akan N410 a bana kuma an bayar da ita akan N456 wanda ko shakka babu zai shafi aikin Hajji.

Muhammad Abba Danbatta ya kara da cewa baya ga tsadar Dalar, tsadar masauki akasar ta Saudiyya ya sabba tashin farashin aikin Hajji.

Ya ce a bara an karbi hayar masukin alhazai  ga kowanne maniyyaci akan Riyal 2,000 yayinda abana ya kai riyal 3,200.

“A bara hatta shi kansa Muhallin da alhazai suka zauna an karbe su akan Riyal 2000 kacal, amma a bana duk tarayyar Najeriya mafi kankantar abinda aka karba inajin 3,300 ne, kuma muhalli ne masu nisa ga yan kudancin kasar nan.

Ya kara da cewa kowanne maniyyaci da zai fito daga Arewacin kasar nan za a biya masa Riyal 3,500 mai makon Riyal 2000 da aka biya a bara.

Muhammad Abba Danbatta ya kara da cewa karuwar Farashin Jaka ma na daya daga cikin abinda ya ta’azzara farashin a bana.

Baya ga jaka shima kayan sawa na Uniform da a ke baiwa alhazai ya karu da N300 akan na bara.

Latest stories

Related stories