Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZaben Gwamnan Kano: Mun Koyawa Ganduje Darasin Siyasa – Kofa

Zaben Gwamnan Kano: Mun Koyawa Ganduje Darasin Siyasa – Kofa

Date:

Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji a jam’iyyar NNPP Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka bar jam’iyyar sun koyawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje darasin siyasa.

 

Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.

 

Idan za a iya tunawa Jam’iyyar NNPP ta doke jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, inda Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben.

 

Ya ce, akwai mutane da gwamna Ganduje ya nuna wa kiyayya, wanda har ta ga sun fice daga jam’iyyar, amma yanzu gas hi sun yi nasarar lashe zabe a jam’iyyar adawa.

 

Ya kara da cewa nasarar da NNPP ta samu na lashe mafi yawan kujerun majalisar tarayya da majalisar jiha ya nuna cewa sun yi wa Ganduje ritayar siyasa.

 

A cewar Kofa “Mun gama da babin siyasar Ganduje domin kuwa mu ke da ranjaye ta ko wane bangare, don haka yanzu babu jam’iyyar APC a Kano.

 

Latest stories

Related stories