Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoShawarar Abba Kabir Yusuf ga Kanawa bata sabawa doka ba-Barr Chedi

Shawarar Abba Kabir Yusuf ga Kanawa bata sabawa doka ba-Barr Chedi

Date:

Wani masanin doka, Barista Ibrahim Abdullahi Chedi, ya ce, shawarwarin da gwamna mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ke ba al’ummar jihar Kano ba su ci karo da tanadin dokar kasa ba.

Wannan na zuwane bayan da hankalin jama’a ya karkata kan yadda ya ke fitar da sanarwa dauke da shawarwari tun bayan da ya karbi takardar shaidar zama zababben gwamna.

Barista Ibrahim, ya kuma ce babu wani laifi a shari’ance, illa dai dama ce ga wanda aka ba shawara ya ci gaba, ko ya tsaya.

Tun bayan fara bayar da shawarar dai cecekuce ya barke a kafafen sada zumunta Inda wasu ke ganin cewa bai kamata zababben gwamnan ya rika irin wadanan magangan ba, sai ya jira sai an rantsar da shi.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...