Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Jigawa ta yankewa yan fashi uku hukuncin kisa

Kotu a Jigawa ta yankewa yan fashi uku hukuncin kisa

Date:

Wata babbar kotu a garin Kaugama da ke jihar Jigawa ta yankewa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin kisan kai da aikata fashi da makami.

Kotun dai ta tabbatarwa Sulaiman Bello, da Auwalu Muhammad, da Yakubu Muhammad laifin kashe Audu Saje, mazaunin kauyen Manda a karamar hukumar, sannan suka gudu da babur din sa.

Bayan wannan, kotun ta same su da laifin sace wata mata, Hadiza Abdullahi a garin Marma da ke yankin karamar hukumar Kirikasamma, sannan suka nemi a biya su fansar Naira milyan dari da hamsin.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Maishari’a M. M. Kaugama, ya ce masu shigar da kara, bisa jagorancin babban lauyan gwamnatin jihar Jigawa sun gamsar da kotun cewa mutanen da ake zargi sun aikata laifukan.

Sai dai kotun ta saki Ya’u Maihatsi, wato mutum na biyu cikin wadanda ake zargi bayan da ta wanke shi daga dukkan zargi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...