Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya zata samar da sabbun gandun daji guda goma a fadin...

Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbun gandun daji guda goma a fadin kasar nan

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince wajen samar da gandun daji goma a sassan kasar nan bayan wani kudirin majalisar wakilai da ya bukaci haka.

Wannan ya biyo bayan kudirin da shugaban masu rinjaye na majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa ya gabatar, inda ya ce shugaban kasa ya sanya hannu kan odar samar da gandun dajin goma ranar 16 ga watan Nuwamban bara.

Za ayi gandun dajin a Falgore dake nan Kano, da Allawa a jihar Neja, da Apoi Forest Reserve a jihar Bayelsa, da Edumenum Reserve a Bayelsa, da dai sauran wurare.

Umar Saleh Anka, daga kungiyar dake rajin kare muhalli ya shaidawa premier radio matukar gwamnatin tarayya ta samar da kwararun ma’aikatan da zasu iya kula da sabbun gandun dajin zai taimaka matuka wajen bunkasa muhalli, tsaro da ilimin magungunan gargajiya da tsirrai

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...