Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mika Mulki Ga Gwamna Maj Jiran Gado.

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mika Mulki Ga Gwamna Maj Jiran Gado.

Date:

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mutane 17 da zasu mika mulki ga sabuwar gwamnati mai jiran gado.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba, ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai bayan zaman majalisar na wannan makon da ya gudana yau a fadar gwamnatin Kano.

Muhammad Garba, ya ce an nada sakataren gwamnati Alhaji Usman Alhaji a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban ma’aikatan jihar Kano, Usman Bala da kwamishinonin shari’a, yada labarai, muhalli, kasuwanci, kasafi da tsare tsare, kanannan hukumomi, ayyuka, kudi da ilimi.

Ya kara da cewa an kuma kafa kwarya kwaryan kwamiti na mutane 100 da ya kunshi daraktoci da shugabanin ma’aikatu daban daban.

Ya ce aikin kwamitin shine tattara bayanai na ayyukan gwamnati domin mikawa sabuwar gwamnati mai kamawa.

Muhammad Garba, ya ce gwamna mai jiran gado zai bada wakilan sa guda uku don sanya su a cikin kwamitin mika mulki da majalisar zartaswar ta kafa.

Ya kuma za a kaddamar da kwamitin a ranar Talata mai zuwa da karfe biyu na rana a fadar gwamnatin Kano.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...