Karibullah Abdulhamid Namadobi
Gwamnatin Kano ta amince da nadin tsohon shugaban jami’ar Bayero kuma tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar jamiāar Ilmi ta Sa’adatu Rimi da aka samar a jihar Kano.
Majalisar zartarwar Kano ta kuma amince da nadin Oba Moshood Aliiwo, Olubadan na Ibadan a matsayin Uban jami’ar ilimi ta Saāadatu Rimi .
Kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar zartarwa da aka gudanar a Kano.
Ya ce hakan ya biyo bayan samun lasisin aiki ne daga hukumar kula da jamiāoāi ta kasa NUC, wacce ta amince da ita a matsayin jamiāar Jiha ta 61 kuma jamiāa ta 222 a tsarin jamiāoāin kasar nan.
Sauran āyan majalisar zartarwar jami’ar sun hada da Dr Muhammad Kwankwaso, Hajiya Zulaiha Ahmed, Dr Ibrahim Wunti, Dr Halima Muhammad da Alhaji Sabiāu Bako.
Ya ce nadin ya zo daidai da sashe na uku na 22 na dokar Jamiāar Ilimi ta Saāadatu Rimi da hukumar