Karibullah Abdulhamid Namadobi
kungiyar kwararrun likitocin zuciya da jijiyoyin jini ta kasa (ACTSON) ta ce fiye da ‘yan Ć™asar 80,000 ne ke bukatar tiyatar zuciya a kowacce shekara.
Shugaban kungiyar Dr. Uvie Onakpoya, ne ya bayyana haka a baban birnin tarayya Abuja a lokacin taron kungiyar na shekara-shekara.
Ya ce cutukan da ke da alaka da zuciya da jijiyoyin jini ne ke kan gaba wajen haddasa yawan mace-mace fiye da kowacce cuta a duniya.
Dr. Onakpoya ya ce yara takwas cikin kowanne 100 da aka haifa na dauke da cutukan da suka shafi zuciya.
Ya kara da cewa a Najeriya fiye da yara 55,000 ake haifa da cutar zuciya a kowacce shekara.