Mukhtar Yahya Usman
Ƙungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta kara tsawaita yajin aikin da take gudanarwa.
Matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi ranar Litinin game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati.
An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja.
Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni tana gudanar da yajin aikin da ya tilastawa ɗaliban jami’oin gwamnati zama a gida.
ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne hanyar samun mafita ga tarin buƙatun da ta gabatar wa gwamnatin Najeriya ciki har da batun inganta musu albashi.