Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniReal Madrid ta lashe Super Cup Karo na biyar

Real Madrid ta lashe Super Cup Karo na biyar

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar cin kofin gwani na gwanaye na UEFA Super Cup, bayan doke Eintracht Frankfurt a wasan karshe a ranar Larabar nan da ci 2-0.

 

Katafaren filin wasa na Olympic dake birnin Helsinki na kasar Finland ne ya karbi bakuncin fafatawar data gudana a daren Larabar 10 ga Agusta.

 

Alkalin wasa Michael Oliver dan kasar Ingila dai shine ya jaboranci wasan karshen da kungiyoyin kasar Spain da Jamus suka fafata.

 

Dan wasa David Alaba ne dai ya fara zura kwallon farko a wasan a minti na 38, bayan samun tai mako daga hannun Casemiro.

 

Sai kuma dan wasa Karim Benzema da ya kara kwallo ta biyu a minti na 65, bayan samun tai mako daga Vinicius Junior.

 

Gasar Super Cup ta shekarar 2022, itace karo na 47 jumulla, da Kawo yanzu Madrid ta lashe gasar sau biyar a tarihi a shekarun 2002, 2014, 2016 da kuma 2017.

 

Hakan da ke nuna yadda Madrid ta kamo Barcelona da AC Milan a yawan lashe gasar ta Super Cup.

Wannan gasa dai ana shiryata ga kungiyoyi biyun da suka lashe manyan gasa a nahiyar turai.

 

Wato Real Madrid data lashe gasar cin kofin turai Champions League, bayan doke Liverpool a wasan karshe.

 

Sai kuma Eintracht Frankfurt data ta lashe gasar Europa ta shekarar da ta gabata bayan doke Rangers.

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...