Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGobara ta kone babban bankin kasa CBN

Gobara ta kone babban bankin kasa CBN

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Wata gobara ta kone wasu sassa na babban bankin kasa (CBN) dake Makurdi a jihar Benue.

Lamarin dai ya faru ne a safiyar Alhamis din nan a bankin dake kusa da fadar gwamnatin jihar ta Benue a Makurdi.

An nada Sheikh Nuru Khalid sabon limamin Juma’a a Abuja

Da yake tabbatar da al’amarin shugaban hukumar kasha gobara ta jihar Donald Ikyaaza, ya ce jami’an su sun kashe gobarar cikin gaggawa.

Sai dai mai Magana da yawun bankin a jihar ta Benue Osita Nwanisobi, ya ce wutar batayi wani tasiri ba kuma babu abin da aka rasa a sanadiyar gobarar.

Ya kuma ce tuni aka cigaba da gudanar da ayyuka kamar yadda aka saba.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma.

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma.

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...