33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAddiniAn nada Sheikh Nuru Khalid sabon limamin Juma'a a Abuja

An nada Sheikh Nuru Khalid sabon limamin Juma’a a Abuja

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...
Mukhtar Yahya Usman
Sabon Masallacin Juma’a da ke unguwar bayan babban bankin kasa CBN ya nada sheikh Nuru Khalid babban limamin Masallacin.

Wannan na zuwa ne awannin kadan bayan da kwamitin Masallacin Juma’a na APO ya Kori Malamin baki daya.

Kwamitin Masallacin ya zargi Malamin da gudanar da hudubar da za ta tada hankulan jama’a.

A cewar shugaban kwamitin Masallacin Sanata Dan Sadau, sun kori Malamin ne saboda kin nuna nadamarsa bayan da aka dakatar da shi.

Sai dai jim kadan bayan korar tasa ne malamin ya samu sabon aiki da Masallacin da ke unguwar babban bankin kasa CBN.

Ana sa ran zai kama aiki a ranar Juma’a mai zuwa 8 ga Aprilu, Inda zai jagoranco Sallar Juma’a.

Latest stories