24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKebbi 2023: Ban kaddamar da takarar neman gwamnaba-Malami

Kebbi 2023: Ban kaddamar da takarar neman gwamnaba-Malami

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Attorney janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya musantan rahoton da ke cewa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Kebbi.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in yada labaransa Umar Jibril Gwandu ya fitar ranar Talata.

Ya ce ya zama dole ya fito ya gayawa al’umma cewar batun ya kaddamar ta takara labarin kanzon kurege ne kawai.

Sanarwar ta ce batun tsayawa takara ba abu ne kankanin ba da har sai wasu yan jarida su fitar ba wai aji daga bakinsaba.

A don hakan ne ma ya nemi jama’a da su yi watsi da jita jitar, su kuma jira abinda zai ce a nan gaba.

Idan za a iya tunawa an dade ana ta yada jita-jitar cewa malamin ne zai gaji gwamnan jihar ta Kebbi Abubakar Atiku Bagudu.

Sai dai da safiya Talatar nan ne wasu jaridu suka wallafa cewar ministan ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar, al’amarin da ya musanta.

Latest stories