Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGanduje ya ki amincewa da murabus din Baffa Babba Dan Agundi

Ganduje ya ki amincewa da murabus din Baffa Babba Dan Agundi

Date:

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yaki amincewa da murabus din shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan Agundi.

Idan za a iya tunawa dai a yau Litinin ne Baffa Babba Dan Agundi ya mika takardar murabus daga mukaminsa ga gwamnatin Kano.

Wannan dai ya biyo bayan umarnin da majalisar tarayya ta fitar kan gyaran Kundin Zaɓe na shekara ta 2022 da cewa, duk mai sha’awar yin takara dole ne ya sauka daga kan muƙaminsa wata guda kafin zaɓen Firamare.

Sai dai bayan mika takardar ne mukaddashin gwamnan Nasiru Yusuf Gawuna yaki amincewa da murabus din.

Haka kuma gwamna Ganduje ya bada umarnin jinkirta karɓar takardar.

Ya kuma umarceshi da ya ci gaba da zama a kan kujerarsa, ya jira umarni na gaba.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi da ta gabata ne shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa yau Litinin zai ajiye muƙaminsa domin tunƙarar al’amuran siyasa gadan-gadan

Shugaban Hukumar ta KAROTA ya bayyana cewa shi mai biyayya ne ga umarnin Gwamna, hakan ta sa ya jinkirta sauka daga kan muƙamin nasa kamar yadda aka bashi umarni.

Latest stories

Related stories