Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan sanda a Kano sun harbe yan ta'adda uku a Tudun Wada

‘Yan sanda a Kano sun harbe yan ta’adda uku a Tudun Wada

Date:

Rundunar ‘yan sandan Kano ta harbe masu gurkuwa da mutane 3 a karamar hukumar Tundun Wada.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Premier Radio ranar Lahadi.

Kiyawa ya ce a cikin daren ranar Asabar ne rundunar ta samu rahoton ‘yan bindiga sunyi garkuwa da wasu yan mata biyu, yayan mutum daya.

Yan bindigar sun shiga kauyen Katsinawa ne suka kuma sace yayan wani mai suna Elesha Aminu suka kuma gudu da su zuwa dajin Falgore.

Yan Matan su ne Zainab Elesha mai shekaru 16 da kuma Nafisa Elesha mai shekaru 18.

A cewarsa bayan samun rahoton ne kuma yan sanda tare da yan sa kai suka shiga dajin na Falgore suka kuma yi musayar wuta da yan ta’addan.

Ya yin musayar wutar rundunar ta yi nasarar kashe mutanen uku tare da kubutar da ‘yan matan da suka sace.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...