Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHarin Jirgin kasa: Har yanzu ba a ga mutum 21-NRC

Harin Jirgin kasa: Har yanzu ba a ga mutum 21-NRC

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta NRC ta ce har yanzu ba a ga mutum 21 daga cikin wadan hadarin jirgin Kasan Kaduna Abuja ya rutsa da sub a.

Babban daraktan hukumar Injiniya Okhiria Fidet ne yabayyana hakan cikin bayanin farko na rahoton hadarin da hukumar ta tattara.

Ya ce binciken nasu ya gano cewa a hukumance fasinjoji 362 ne cikin jirgin da hadarin ya rutsa dasu.

Injiniyan ya kara da cewar kawo yanzu sun tabbatar da cewa fasinjoji 170 sun tsira, yayin da 21 suka bace, sai dai bai yi karin bayani akan ragowar fasinjoji 171 ba.

Idan za a iya tunawa dai a ranar litinin din makon jiya ne yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna da ya yi sanadiyyar hallaka wasu mutane tare da jikkta wasu da dama.

Haka kuma rahotanni farko sun ce mutane sama da dari tara ne cikin jirgin, sai dai rahoton ya ce jirgin ma zai iya daukar mutane 840 ne kawai

Tuni dai aka dakatar da jigilar jiragen kasa a tsakanin birnin na Abuja da Kaduna, har zuwa lokacin da za a kammala gyara titin da ‘yan ta’adda suka dasawa bam, da kuma tabbatar da tsaro.

Latest stories

Related stories