Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniAn dakatar da limami saboda caccakar Buhari

An dakatar da limami saboda caccakar Buhari

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kwamitin Masallacin Apo da ke birinin tarayya Abuja yadakatar da babban limamin masallacin jumaá na APO Sheikh Nura Khalid bisa caccakar gwamnati.

An dai jiyo Dr Nura Khalid cikin hudubar da ya gabatar a jumaár da ta gabata yana caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matsalar tsaron da ke addabar kasar nan.

A hudubar tasa ya ja hankali matasa da su kauracewa fita zabe idan har gwamnati ta gaza magance matsalar tsaron.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda daya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zabe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” inji Sheikh Nuru Khalid a hudubar tasa.

Sai dai a cikin wani sako da shugaban kwamitin Masallacin, Sanata Sa’idu Muhammed Dansadau ya fitar ta ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a.

Sanarwar ta ce, “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ’yan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.

“An dauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’ ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ’yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.

“Ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da wadanda suka saba wa Allah, da masu zabe da kuma kasa,”

Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta saba wa addinin Islama.

Kazalika, a cikin sanarwar, kwamitin ya nada sabbin lamamai na Masallacin inda Malam Mohammad zai yi tafsiri, yayin da kuma Malam Abdullahi zai jagoranci Juma’a.

Latest stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...