Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiINEC: Zata rufe yin rijistar katin zabe

INEC: Zata rufe yin rijistar katin zabe

Date:

Hukumar zabe ta kasa (INEC) tace za a rufe yin rijistar katin zabe a kasar nan daga ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya fitar a Larabar nan a Abuja.

Najeriya ta dauko hanyar rugujewa-Jega

Farfesa Mahmood, ya ce mutane miliyan daya da goma sha hudu da dari uku da biyu (1,014,382) ne sukayi rijista ta yanar gizo yayin da mutane miliyan daya da hamsin da tara da saba’in da shida (1,509,076) sukayi rijista a guraren da hukumar ta samar.

Shugaban ya kuma ce mutane miliyan shida da saba’in da daya da dubu dari da shida (671,106) ne suka mika bukatar yin gyare gyare ko sabunta katin zaben nasu.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ba za a sauya lokacin da aka saka don gudanar da babban zaben badi dake tafe ba a don haka ya gargadi masu ruwa da tsaki dasu hada hannu da hukumar don samun nasarar shirye shiryen zaben.

Idan za a iya tunawa dai tun a watan Yunin shekarar data gabata ne hukumar zaben ta INEC ta sanar da fara yin rijistar katin zaben a fadin kasar nan.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...