Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiPremier Radio ta samu mabiya miliyan daya a Youtube

Premier Radio ta samu mabiya miliyan daya a Youtube

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

A yau ne, Alhamis 21ga watan Aprailu, shafin YouTube na Premier Radio ya sami ziyara da bibiya na sama da mutane miliyan daya.

A halin yanzu da muke wannan rahoto an kalli wannan shafi namu na sada zumunta na YouTube sau 1,010,158.

Wannan babban cigaba ne ga Premier Radio in anyi la’akari da cewa wannan nasara ta samu ne a yan watanni kalilan da fara wallafa rahotannin mu a YouTube.

Gidan Rediyon Premier na mika godiya ga dubban Jama’a da suke bibiyar shafukanmu na sada zumunta musamman na YouTube da Facebook.

Babu shakka wannan nasara ta samu ne saboda hadin kai da gudunmowa da kuke bamu wajen bibiyar labarai da rahotannin mu.
Muna tabbatar muku da cewa za mu cigaba da gabatar muku da rahotanni masu inganci da ma’ana.

Da fatan za’a cigaba da bin shafukan mu na sada zumunta kamar haka:
YouTube: #premier radio
Facebook: Premier Radio 102.7fm
Instagram:#premierradio.ng
Twitter: @premierradio.ng
LinkedIn:@premierradio.ng

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories