Kungiyar malaman jam’I’o ta kasa ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta bata naira biliyan dari biyu daga cikin naira tiriliyan hudu da take nema don janye yajin aikin da takeyi.
Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce gwamnatin tarayya ta nuna cewar bata da niyar magance matsaloli kungiyar da ya tilastawa dalibai zama a gida.
Shugaban ya bayyana hakane a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan talabijin na Channels.
Kungiyar ASUU ta fara yajin aiki ne a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata inda take neman gwamnati data cika alkawarin da tayi da ita tun a shekarar 2009.
Ya ce gwamnati ta magance matsalar tallafin man fetur da naira tiriliyan hudu amma ta gaza magance matsalar ilimin kasar nan.
Ya ce idan da gwamanti zata baiwa kungiyar naira biliyan 200 daga cikin tiriliyan 4 hakan zai sa kungiyar tazo da mafita kan batun yajin aikin.