Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGadar Lado ta bule dake Gyadi-gyadi

Gadar Lado ta bule dake Gyadi-gyadi

Date:


A karo na biyu gadar Ado Bayero da aka fi sani da gadar Lado dake kan titin Zaria ta sake bulewa.

A kwanakin baya ma gadar ta bule amma akai gaggawar gyarata cikin kankanin lokaci.

Sai dai a wannan karon ba a hangi ma’aikatan kamfani dake kula da gadar ba a wurin haka zalika gadar ta sake bulewa ne a dai dai inda akai gyara a baya.

Bulewar gadar dai ya tilastawa masu ababen hawa kaucewa cikin gaggawa don gudun gamuwa da tsautsayi.

Gwamnatin Kano zata siyawa Katsina United sabuwar mota

Idan za a iya tunawa dai Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Bashir Garba Lado ne ya kawo aikin gina gadar inda kuma kamfanin Rocad Construction Ltd ya gina gadar a shekara 2015 kan kudi miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar.

Latest stories

Related stories