Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaTinubu ya haramtawa dukkan jami’an gwamnatinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje

Tinubu ya haramtawa dukkan jami’an gwamnatinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje

Date:

Shugaba Tinubu ya haramtawa ministoci, Shugabannin hukumomi da sauran jami’an Gwamnati tafiye-tafiyen Zuwa kasashen waje.
Sabon umarnin na kunshe cikin wata takarda da aka aikewa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.
Takardar mai dauke da sa hannun shugaban ma’akatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ta ce matakin zai yi aiki ne na tsawon wata uku daga ranar 1 ga watan Aprilu mai kamawa.
Tinubu ya jaddada cewa dole ne jami’an gwamnati da suke da niyyar yin tafiya zuwa kasashen waje su samu amincewar shugaban kasa, akalla makwo biyu kafin tafiyar, wanda hakan ya zama doka daga yanzu.
Ya ce hakan ne zai sa a duba domin ganin muhimmancin tafiyar kafin amincewa da ita.
Sai dai tafiye-tafiyen sun shafi iya wanda gwamnati za ta dauki nauyi da kudinta, ba wai na kashin kai ba.

Latest stories

Related stories