Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin bayani kan fargabar juyin...

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin bayani kan fargabar juyin mulki da ake rade-radi

Date:

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin bayani game da fargabar juyin mulki da ake rade-radi a sassan kasar nan.

Babban Hafsan sojin kasan, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana hakan a cikin makalar da ya gabatar yayin wata laccar da rundunar ta gudanar a shalkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja.

Lagbaja ya jaddada cewa rundunar sojin za ta ci gaba da kare kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, haka kuma, ba za ta sauya wannan akida ba ko tunanin kawo wa tsarin wata tangarda saboda wani dalili.

Ya kuma bukaci sojojin kasar nan da su kasance masu kwazo da kwarewa sannan su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu bisa tsarin mulki.

A bayan nan ne rundunar sojin kasar nan ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta.

A sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta ce dakarunta ba su da wata aniya ta karɓe ragamar iko daga tsarin mulkin dimokuradiyya, tana mai cewa tsarin dimokuradiyya zama daram.

Latest stories

Related stories