Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTarihi zai yi min adalci-Buhari | Premier Radio | 27.01.2023

Tarihi zai yi min adalci-Buhari | Premier Radio | 27.01.2023

Date:

Ibrahim Hassan Hausawa

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana amannarsa wajen cewa tarihi zai musu adalci domin sanya su cikin wadanda zai dinga tunawa da su, musamman idan aka yi duba dangane da tarihin yadda suka gaji kasar.

 

Shugaba Buhari a cewarsa wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Femi adesina ya fitar, jamiyyar APC ta samu mulkin kasar nan a lokacin da take cikin yanayi na fama da matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

 

Shugaba Buhari yayin ziyarar kaddamar da wasu ayyuka da yake yanzu haka a jihar Katsina gwamnatinsa tayi iya abinda zasu iya wajen samar da sassauci dangane da hain da suka samu kasar.

 

Daga nan sai ya yabawa gwamna Aminu Masari bias yadda ya samar da managartan ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta samar a jihar, wanda yace yana da tabbacin alummah zasu amfana da su matuka.

 

A yayin ziyarar shugaban kasar a jihar Katsina ya kaddamar da wasu ayyuka da suka hadar da babban asibitin jihar, sai kuma wata gadar sama ta farko wadda itama gwamna Masari ya samar da ita, wadda yanzu haka ta kamala da kusan kaso 90.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...