Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNRC ta dakatar da jirgin kasan Abuja Zuwa Kaduna

NRC ta dakatar da jirgin kasan Abuja Zuwa Kaduna

Date:

Hukumar kula da jiragen kasa ta kasa(NRC) ta dakatar da jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon gocewa daga layin dogo da wani jirgi ya yi a ranar Juma’a.

Daraktan NRC Niyi Alli ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Mista Alli yace “Da Taimakon Ubangiji ba a samu wanda ya yi rauni ba ko daya, sai dai duk da haka muna neman afuwar al’ummar da wannan tsaiko na jigilar jirgin zai shafa”

Ya kuma tabbatar da cewa tuni hukumar NRC ta fara kokarin shawo kan matsalar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan dawo da zirga-zirgar jirgin tun bayan dakatar da shi sakamakon sace fasinjojin da ’yan bindiga suka yi a watan Maris na bara.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories