Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSauyin kudi: Wani lauya ya kai CBN kara kotu | Premier Radio...

Sauyin kudi: Wani lauya ya kai CBN kara kotu | Premier Radio | 27.01.2023

Date:

Abdurrashid Hussain

 

Wani lauya Joshua Alobo ya shiga da kara babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ya roki kotun da ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga daina karɓar tsoffin takardun Naira daga ranar 31 ga watan Janairu.

 

Alobo ya kuma roki kotun da ta bayar da umarnin tsawaita wa’adin lokacin da tsofaffin takardun za su daina amfani har na tsawon makonni uku.

 

Ya ce hakan ya kasance don a ba da lokacin da bankunan kasuwanci za su sami isassun sabbin takardun kudi da za su fitar ga al’umma.

 

A cikin takardar ƙorafin, wadda ya shigar ta hannun Musa Damudi, lauyan ya shaida wa kotun cewa Gwamnan CBN a ranar 26 ga Oktoba, 2022, ya sanar da cewa babban bankin zai buga sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 da aka sake fasalin a cikin tsarin hada-hadar kudi.

 

Ya ce matakin, duk da cewa an yi maraba da shi, ya haifar da tashin hankali a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman ma masu karamin karfi saboda har yanzu ba su samu damar yin amfani da sabbin takardun kudi na Naira ba.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...