Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJigawa: ‘Yan kasuwa sun rufe shagunansu saboda karancin sabon kudi

Jigawa: ‘Yan kasuwa sun rufe shagunansu saboda karancin sabon kudi

Date:

Wasu ’yan kasuwa a jihar Jigawa sun rufe shagunansu   saboda karancin sabbin kudin Naira.

 

Hakan ya biyo bayan sanarwar da babban bankin Najeriya CBN ya bayar na cewa ranar 31 ga watan Janairu ya rage wa’adin daina amfani da tsofaffin kudaden Naira a fadin kasar.

 

Wasu ‘yan kasuwa a Birnin Dutse sun shaidawa jaridar Daily Post cewa  ba su da wani zabi da ya wuce su rufe shagunansu har sai sabbin kudi sun wadata.

 

Wani dan kasuwa da ke da kantin sayar da kayayyaki a Yelwawa Quaters a cikin birnin Dutse, Malam Musa, ya ce ya rufe shagonsa ne saboda rashin samun sabbin takardun kudi na Naira.

 

“Na kasance ina yin tallace-tallace kusan Naira 200,000 a kowace rana amma da kyar aka samu Naira 10,000 sabbin takardun kudi, kuma duk lokacin da na karba tsohon na kan yi wahala in canza shi a bankina saboda doguwar layukan da ake yi.” Inji shi.

 

Haka kuma, wata mai sayar da takarda da pap tare da Gida Dubu a Dutse, Bintu Samuel, ta ce ta rufe kasuwancin ta har sai bayan an fara zagawa da sabbin takardun Naira.

 

DAILY POST ta ruwaito cewa lamarin na ci gaba da kawo tsako ga harkokin kasuwanci a jihar ta Jigawa.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...