Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJihar Katsina ta bada hutun kwanaki 2 saboda ziyarar Buhari

Jihar Katsina ta bada hutun kwanaki 2 saboda ziyarar Buhari

Date:

Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana ranar Alhamis 26 ga wata da kuma Juma’a a matsayin ranakun hutu, domin bai wa ma’aikata damar tarbar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a ziyarar da zai yi ta kwana biyu a jihar.

 

Sanarwar da babban sakataren ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu na jihar Sani Bala Kabomo ya fitar, ya ce hutun da aka bayar zai taimakawa ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi da sauran al’umma damar yi wa Shugaba Buhari barka da zuwa.

 

Ya ƙara da cewa hutun ba zai shafi mai’akatan ayyukan tarayya da na bankuna da sauran masu ayyuka na musamman.

 

Ziyarar ta Shugaba Buhari zuwa Jihar ta Katsina na zuwa ne kwanaki kadan kafin ziyarar da Shugaban kasar zai kawo nan Kano a ranakun Litinin 30 ga watan Janairu da Talata 31 ga watan, inda shugaba Buhari zai kammadar da wasu muhimman ayyuka.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...