Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Buhari ya amince da dage ranar kidayar alumma

Shugaba Buhari ya amince da dage ranar kidayar alumma

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar jama’a da gidaje wadda aka yi niyyar gudanarwa daga 3 zuwa 7 ga watan Mayun 2023.

Ma’aikatar yada labarai da al’adu ta kasa ce ta sanar da hakan a wata sanarwar da ta fitar a Asabar dinnan.

Ma’aikatar ta bayyana cewa sabuwar gwamnatin da za ta gaji mulki za ta sanar da sabon jadawali da kuma ranakun da za a gudanar da kidayar.

A jiya Juma’a ne shugaban hukumar kidaya ta kasa, Nasir Isa Kwarra ya kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ba shi bayanai kan halin da ake ciki kan batun shirye-shiryen kidayar.

Sai dai a sanarwar da gwamnatin ta fitar, ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja ba kan dalilin da ya sa aka dage kidayar ba, sai dai a kwanakin baya an ta rade-radin cewa akwai yiwuwar a dage ta saboda wasu shirye-shirye da ba a kammala ba.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya yaba da irin tsare-tsaren da hukumar kidayar ta fito da su musamman samar da kayayyakin kimiyya wadanda za su iya gudanar da kidaya da za a yi alfahari da ita a duniya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...