Jamâiyyar PDP ta bukaci hukumomin kasa da kasa su kakabawa shugaba Buhari takunkumin tafiye tafiye bayan mika mulki.
Tace matakin zai zamo sakamakon abinda ya shuka na durkusar da tsarin dimokradiyyar Najeriya.
Wannan na a matsayin martani ga kalaman shugaban, wanda yace PDPn ta fadi zabe ne a 2023, sabida ci da zuci.
To sai dai, a taron manema labarai da ta gudanar a sakatariyar ta ta kasa, sakataren yada labaran ta Mr Debo Ologunagba, yayi ikirarin cewa duniya ta yiwa zaben bana lamba a matsayin mafi muni a tarihin kasarnan.
Tace zaben cike yake da almundahana, da kuma karya dokokin INEC, baya ga sauya sakamako da na bogi, abinda ya baiwa APC damar samun nasara.
